Monday, December 16
Shadow

Ku Janye yajin aikin da kuke ku rungumi Sulhu da gwamnati>’Yansanda suka roki kungiyar NLC

Hukumar ‘yansandan Najeriya sun roki kungiyar kwadago ta NLC da ta rungumi sulhu ta janye yajin aikin data shiga.

Hukumar a wata sanarwa data fitar tace tabbas kungiyar kwadago ta NLC na da ikon shiga yajin aikin amma ya kamata a bi dokar da kasa ta tanadar dan kaucewa take doka da oda.

Hukumar ‘yansandan tace wannan yajin aikin zai jawo fargaba da kuma dumamar yanayin siyasa.

Dan hakane ‘yansandan ke kira da NLC ta janye yajin aikin ta koma teburin sulhu da gwamnati.

Hukumar ‘yansandan ta kuma baiwa jama’a tabbacin samar da tsaro inda tace ta kai jami’anta gurare da yawa dan tabbatar da ba’a karya doka ba.

Karanta Wannan  Kungiyar 'yan kasuwar man fetur, IPMAN ta yi baranzanar tsayar da aiki saboda karin kudin man feturninda tace hakan ya kara jefa 'yan Najeriya wahala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *