
Tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki ya jawo hankalin kakakin majalisar na yanzu, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti da su kai zuciya nesa kada su yi abinda zai zubarwa da majalisar dattijai mutunci a Idon Duniya.
Bukola Saraki yace duk wanda ya taba zama sanata ko yayi aiki a majalisar ba zai so a bata mata suna ba.
Ya jawo hankalin cewa a kafa kwamiti na musamman da zai binciki kowane bangare ba tare da nuna banbanci ba yanda za’awa kowa adalci.
Ya bayar da misalin cewa shima sanda yana kakakin majalisar akwai wani sanata da ya zargeshi da cewa ya siyo mota ba tare da biyan kudin harajin Kwastam ba amma da yake yasan yana da gaskiya, sai yace a yi binciken a gaban jama’a inda aka gayyaci ‘yan jarida ya wanke kansa.
Sanata Natasha Akpoti dai na zargin kakakin majalisar Godswill Akpabio da cewa ya nemi yin lalata da ita ta kiyane ahiyasa yake mata abinda bai dace ba a majalisar.