Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci kungiyoyin kwadago da su saurari Gwamnatin Najeriya domin yajin aikin zai jefa kasar cikin kunci.
Abubakar ya ce bai kamata kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da Takwararta su gaji da tattaunawa da Gwamnati ba.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Sarkin Musulmi ya bukaci kungiyar kwadago da ta janye yajin aikin.
Sarkin Musulmi ya ce, “Ya kamata shugabannin kungiyoyin kwadago su yi la’akari da illar da yajin aiki yake da shi ga jin dadin ‘yan Nijeriya wanda suke iƙirarin don su suke yi da nufin kare muradun ƴan ƙasa, don haka su yi watsi da matakin na shiga yajin aiki.
Muna kira ga kungiyoyin kwadagon da kada su sake jefa al’ummar kasar cikin wani hali na kuncin rayuwa domin abin da zai faru kenan idan suka aiwatar da shirinsu na shiga wannan yajin aikin.
“Ya kamata su yi kokarin sauraron Gwamnati, yayin da Gwamnati ma ya kamata ta saurare su, domin bangarorin biyu su cimma matsayar da za ta kasance mai amfani ga daukacin ‘yan Najeriya.”
Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Daga shafin Dimikradiyya.