
Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, kana kuma ta hannun daman shahararren mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ta nemi afuwar dukkan wanda ta taɓa yi wa ba daidai ba tare da ba wa abokan sana’arta a Kannywood haƙurin rashin gayyatarsu ɗaurin aurenta.
Humaira ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram jim kaɗan bayan ɗaura aurenta da Rarara a wannan rana ta Juma’a a garin Maiduguri, kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
“Ina yi wa dukkan ƴan’uwa abokan sana’ata da abokan arziƙi fatan alkhairi. Ku yi haƙurin rashin sanar muku da ɗaurin aure da ba a yi ba, hakan ya faru ne ba tare da mun shirya ba. An je da niyar saka rana kawai iyaye suka ce a tsaya a ɗaura a hutar da mutane. Daga baya za a sa ranar biki. Za mu gayyaci kowa. A yi haƙuri a yi mana fatan alkhairi”. A cewarta.
Ta kuma ƙara da neman afuwar dukkan wanda ta taɓa yi wa kuskure. “Ni ma na yafe wa dukkan wanda ya yi min wani abu wanda na sani da wanda ban sani ba. Duk na yafe musu Duniya da Lahira”. Inji ta.