
Wani ba’amurke kuma dan Jarida, me suna Ron Filipkowski ya bayyana cewa akwai yiyuwar shugaban kasarsu, Donald Trump na da tabin hankali.
Ya bayyana hakane a yayin da yake martani game da barazanar kawo hari Najeriya da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi.
Barazanar ta Trump dai ta tayar da kura sosai inda akai ta mata fassara daban-daban inda wasu ke ganin ba maganar Khisan Kiristoci ce zata kawoshi Najeriya ba, akwaidai wata manufa.