
Kasar Amurka ta gargadi Najeriya da cewa, Masu ikirarin Jìhàdì na kokarin mamaye kasar.
Amurka tace bama Najeriya kadai ba, masu ikirarin jihadin na son mamaye kasashe irin su Mali, Burkina Faso, da Niger.
Kwamandan rundunar sojojin Amurka dake Africa, Gen Michael Langley ne ya bayyana hakan inda yace Hare-haren masu ikirarin Jìhàdì a Najeriya abin damuwane.
Yace masu ikirarin jihadin nason yin Amfani da yankin kasashen African dan gudanar da safarar makamai da fasa Kwauri.
Yankin na Sahel Africa na daga cikin wanda aka bayyana dake fuskantar mafi munin hare-haren masu ikirarin Jìhàdì.