Friday, December 26
Shadow

Kuma Dai: Gwamnatin Tarayya zata sae ciwo bashin Dala $1.75bn

A yayin da Gwamnatin tarayya tace kudin shigarta daga bangarorin da bana danyen ma fetur ba sun karu da kaso 40 cikin 100, tana kuma kokarin kara ciwo Bashi.

Gwamnatin dai tace duk da wannan kari data samu na kudin shiga, har yanzu tana fama da karancin kudin gudanar da ayyuka.

A baya bayannan, ‘yan kwangila sun gudanar da zanga-zanga inda suke neman a biyansu kudin ayyukan da suka yi a shekarar 2024 da suka kai Naira Tiriliyan 4.

Domin cike gibin wannan karancin kudin, Gwamnatin tarayya na shirin ciwo bashin Dala Biliyan $1.75bn dan gudanar da ayyuka.

Saidai hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa sun samu duka kudin shigar da suke bukata dan gudanar da ayyuka a shekarar 2025, ba zasu kara ciwo bashi ba a wannan shekarar.

Karanta Wannan  Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Biya Duk Kudaden Jinya Na Mutanen Da Hadari Ya Rutsa Da Su Da Motar Gwamna Radda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *