
Jirgin yakin sojojin Najariya ya kashe farar hula 6 a kauyen Zakka dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina bisa kuskure.
Hakan ya farune bayan da wasu ‘yan Bindiga suka kai hari ofishin ‘yansanda suka kashe ‘yansanda 2.
Harin ya farune ranar Asabar data gabata inda sojojin suka wurga bama-bamai akan wasu bukkoki dake wajen garin na Zakka.
Wasu shaidu 3 sun tabbatar da faruwar lamarin ga majiyarmu.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya tabbatar da faruwar lamarin.