
Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, jirgin yakin sojin Najeriya ya kashe ‘yan Bijilante bisa kuskure a jihar Zamfara.
Shafin Bakatsina ya ruwaito cewa, lamarin ya farune a kauyen Mani dake kamar Hukumar Maru dake jihar.
Yace an kashe manoma 50 da yin garkuwa da mutane 20 a ranar da lamarin ya faru bayan harin ‘yan Bindiga.
Yace jirgin da aka kawo dan ya taimaka a yi maganin ‘yan Bindigar sai ya kare da kashe ‘yan Banga bisa kuskure.
Zuwa yanzu dai Gwamnatin jihar Zamfara da Hukumomin tsaro basu ce uffan ba kan lamarin.