Sunday, March 23
Shadow

Kuma Dai: Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila inda ta yiwa Sanata Godswill Akpabio tonon silili.

A can ma dai ta sake bayyana yanda Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata.

Ta musanta ikirarin Majalisar Dattijai na cewa an dakatar da itane saboda rashin biyayya ga dokokin majalisar inda tace me yasa sai da ta gabatar da korafi akan sanata Godswill Akpabio ne sannan za’a dakatar da ita?

Sanata Natasha ta bayyana cewa ta yi ta kai korafi dan neman yiwa mutanenta aiki amma sai sanata Godswill Akpabio yaki amincewa.

Tace har mijinta saboda abokin Sanata Godswill Akpabio ne ya rika rokonsa akan ya amince da wasu kudirori data kai majalisar amma ya kiya sai yace sai nan gaba.

Karanta Wannan  Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *