Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi.
Wannan shine tayi na 4 da gwamnatin tarayya tawa NLC a cikin watanni 2 da aka shude ana tattaunawar.
NLC dai ta sakko daga bukatar ta ta cewa sai an biya Naira 615,000 a matsayin mafi karancin albashi inda ta nemi yanzu a biya N118,000 zuwa N497,000.
Wakilin NLC, Benson Upah ya bayyana cewa, Gwamnatin ba da gaske take ba da take cewa zata biyasu Naira Dubu sittin(60,000).
Yace Gwamnatin ce ta jawo wannan matsala inda ta kawo tsare-tsare wanda suka saka al’umma cikin wahala