Kungiyar kwadago tace zata nemi a kara mata yawan mafi karancin albashi daga dubu 70 zuwa sama a shekarar 2025.
Kunguyar tace a kowace shekara ya kamata a rika lura da yanayin tsadar rayuwa dan karawa ma’aikata Albashi.
Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan inda yace me zai hana a rika la’akari da yanayin tsadar rayuwa kowace shekara dan karawa ma’aikata Albashi maimakon jira sai bayan shekara 5.
Yace su da NLC sun fara tattaunawa kan maganar.
A watan Yuli da ya gabata ne dai kungiyoyin kwadagon da gwamnatin tarayya suka cimma matsaya game da karin Albashi zuwa Naira dubu 70 maimakon Naira dubu 30 da ake biya a baya.
Hakan na zuwane bayan shekaru 5 da yin karin farko.