Friday, July 17
Shadow

Kungiyar Kwadago tace zata nemi karin mafi karancin Albashi a shekarar 2025 saboda tsadar rayuwa

Kungiyar kwadago tace zata nemi a kara mata yawan mafi karancin albashi daga dubu 70 zuwa sama a shekarar 2025.

Kunguyar tace a kowace shekara ya kamata a rika lura da yanayin tsadar rayuwa dan karawa ma’aikata Albashi.

Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan inda yace me zai hana a rika la’akari da yanayin tsadar rayuwa kowace shekara dan karawa ma’aikata Albashi maimakon jira sai bayan shekara 5.

Yace su da NLC sun fara tattaunawa kan maganar.

A watan Yuli da ya gabata ne dai kungiyoyin kwadagon da gwamnatin tarayya suka cimma matsaya game da karin Albashi zuwa Naira dubu 70 maimakon Naira dubu 30 da ake biya a baya.

Karanta Wannan  A biyamu diyyar Tiriliyan 10 sannan a bamu hakuri, Inyamurai suka gayawa shugaba Tinubu game da maganar kazafin da aka musu na cewa sune suka shirya juyin mulki na farko amma IBB ya wankesu

Hakan na zuwane bayan shekaru 5 da yin karin farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *