Friday, December 5
Shadow

Kungiyar malaman jami’a ta yi barazanar shiga yajin aikin da ba’a taba ganin irinsa ba

ASUU: Mun shirya shiga yajin aikin da ba a taɓa irin sa a Nijeriya ba – ASUU.

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa tana shirye-shiryen shiga babban yajin aiki fiye da duk wanda aka taba yi, muddin gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar 2009 da aka kulla tsakaninta da kungiyar.

Sashen ASUU na Jami’ar Calabar (Unical) ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Calabar, ranar Talata.

Shugaban sashen, Dr. Peter Ubi, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta cika alkawurran da suka dade suna jinkiri, wadanda aka tsara domin inganta matsayin ilimin jami’a a kasar.

Karanta Wannan  Da Duminsa: 'Yansanda a jihar Naija sun yi harbi dan hana masu zàngà-zàngà tare babbar hanya

Ya bayyana cewa za a fara yajin aikin da zarar babban kwamitin ASUU na kasa ya bayar da sanarwa bayan taron da za a gudanar a ranar 28 ga watan Agusta.

Daga cikin bukatun da kungiyar ta jero akwai: sake duba yarjejeniyar 2009, samar da ingantaccen kudin gudanarwa ga jami’o’i, da kuma farfado da jami’o’i.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *