Wednesday, January 15
Shadow

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Ahmad Jalam ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Misau-Darazo ranar Asabar a cewar gwamnatin jihar

Gwamna Bala na Jihar Bauchi Ya Halarci Jana’izar Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Allah Ya Karɓi Rayuwarsa A Daren Jiya

Gwamna Bala Mohammed ya halarci Sallar Jana’izar Marigayi Alh Ahmad Aliyu Jalam Kwamishinan ƙananan Hukumomi na jihar Bauchi wanda ya Rasu a sakamakon hatsarin Mota Daga Bauchi Zuwa Jalam

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana shi a matsayin abokin aiki mai himma da kwazo da bayar da gudunmawar ci gaban Gwamnatin PDP a Jihar Bauchi.

Ya ƙara da cewa Rasuwar Ahmed Aliyu Jalam ta haifar da zullumi tare da yin zaman makoki, yana mai rokon Allah ya ba shi AlJannati Firdausi, ya kuma baiwa iyalansa kwarin guiwar jure wannan babban rashi.

Karanta Wannan  Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

Sai dai ya jajantawa ‘yan uwa da al’ummar Jalam a madadin Gwamnatin jihar da jam’iyyar PDP da daukacin al’ummar jihar Bauchi.

Manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar PDP reshen jihar Bauchi sun halarci jana’izar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *