
Fitaccen ɗan siyasa kuma ɗan gwagwarmaya a Najeriya, Omoyele Sowore ya ziyarci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Sowore ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya sanya hotunan ziyarar sannan ya rubuta cewa, “yau na kai wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yarin Kuje tare da rakiyar Barista Hamza Nuhu Dantani.
“An yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa ne a Kano bisa zarginsa da ɓatanci a zamanin tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje,” in ji shi, inda ya ce ɗaurin na da alaƙa da siyasa.
Sowore ya ce ya yi mamakin yadda, “aka haɗa baki da wasu na kusa da malamin wajen ganin an tasa ƙeyarsa gidan yari.”
Ya ce sun samu malamain cikin karsashi da walwala, “inda ya bayyana mana cewa Allah ne yake tsare da shi, kuma zai ci gaba da riƙo da koyarwar Allah har zuwa ƙarshen rayuwarsa.”
Sowore ya ce babu mutumin da ya cancanci rashin adalci, sannan ya ce dole ne a tabbaar da adalci ga Abduljabbar tare da kawo ƙarshen abin da ya bayyana da amfani da addini da wasu “gurɓatattun ƴansiyasa ke yi.”