
Sabon Ministan tsaro Janar Christopher Musa ya bayar da tabbacin cewa kwanannan cikin gaggawa za’a ga sakamako me kyau.
Ya bayyana hakane a ganawa da manema labarai a Abuja bayan rantsar dashi a matsayin Ministan tsaro.
Yace zai hada kai da dukkan wadanda suka kamata dan tabbatar da an samar da tsaro a Najeriya.