Rahotanni sun ce biyo bayan karuwar yawan man fetur din da kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya sanar da cewa an samu na ganga Miliyan 1.8 duk kullun, yawan kudin da gwamnatin tarayya ke samu zai karu zuwa Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata.
Farashin man Brent yana a matsayin dala $81 kowace ganga. Idan ana samun ganga Miliyan 1.8 kullun hakan na nufin Najeriya zata samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata.
Shugaban kamfanin man fetur dun na kasa, Mele Kolo Kyari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis inda yace yawan man fetur din da Najeriya ke hakowa ya karu.