Monday, December 15
Shadow

An kori malaman jami’a 4 saboda lalata da dalibai mata

Masu gudanarwa na makarantar jami’ar Federal University, Lokoja, dale jihar Kogi, sun sallami malamai 4 daga aiki saboda samunsu da aikata ba daidai ba wajan jarabawa da kuma yin lalata da dalibai mata.

Sun zartar da wannan hukunci ne ranar Alhamis bayan wani zama da suka yi kan batun.

Hakan ya biyo bayan zargin da akawa malaman na yin lalata da dalibai mata da kuma aikata ba daidai ba wajan jarabawa.

Shugaban kwamitin gudanarwar makarantar, Senator Victor Ndoma-Egba ya yabawa wadanda suka yi wannan bincike inda yace sun kyauta da suka bi ka’ida wajan yin binciken.

Yace kuma su gaggauta kammala sauran binciken da ake yo akan malamai.

Karanta Wannan  DA DUMI DUMINSA: fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al'ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu

Ya jawo hankalin malaman kada su saka kansu wajan cin zarafin dalibai sannan ya jawo hankalin daliban da duk wanda aka ci zarafinsa da ya fito ya yi magana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *