Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta bayyana cewa, zata fara nemo man fetur me arha ko da daga kasashen wajene.
Ta bayyana hakane ta bakin kakakinta, Chief Chinedu Ukadike a hirarsa da jaridar Vanguard.
Yace a yanzu tunda NNPCL ba su ne kadai masu shigo da man fetur ba, zasu iya shigo da man fetur dinsu daga duk inda suke so.
Hakan na zuwane bayan da kamfanin na man fetur na kasa, NNPCL ya kara farashin man fetur din zuwa Naira 998 a wasu guraren kuma Naira 1030 akan kowace Lita.