
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin rage farashin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira Dubu 12.
Wannan ragin farashin tuni ya fara aiki a Asibitocin gwamnati dake fadin Najeriya.
Me magana da yawun shugaban kasar, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X.
Yace shugaban yayi wannan ragi ne dan saukakawa masu ciwon koda.
Wasu daga cikin Asibitocin gwamnatin tarayya da suka fara aiwatar da wannan ragi sun hada da Medical Centre (FMC), Ebute-Metta, Lagos; Federal Medical Centre (FMC), Jabi, Abuja; University College Hospital (UCH), Ibadan; da Federal Medical Centre (FMC), Owerri.
Sauran sune University of Maiduguri Teaching Hospital (UMTH), Maiduguri; the Federal Medical Centre (FMC), Abeokuta; Lagos University Teaching Hospital (LUTH), Lagos; Federal Medical Centre (FMC), Azare; University of Benin Teaching Hospital (UBTH), Benin; da University of Calabar Teaching Hospital (UCTH), Calabar.
Yace za’a kara wasu manyan Asibitocin gwamnatin nan gaba kadan kamin karshen shekarar nan da muke ciki.