Monday, January 6
Shadow

Lakurawa sun kashe ƴan sanda biyu, sun yi awon gaba da shanu sama da 500 a Kebbi

Ana ci gaba da samun bayanai game da harin da ƴan ƙungiyar nan ta Lakurawa suka kai garin Na-tisne na yankin ƙaramar hukumar Arugungun ta jihar Kebbi.

Harin wanda suka kai a ranar Alhamis da daddare, ya janyo mutuwar ƴan sanda biyu inda kuma suka kore shanu fiye da 500.

Sai dai an samu nasarar murƙushe maharan, a sakamakon wani ƙoƙari na haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kebbi da jam’an tsaro.

Shugaban ƙaramar hukumar Arugungun ta jihar Kebbi, Honarabul Aliyu Gulma ya shaida wa BBC cewa tun bayan faruwar sojoji da sauran jami’an tsaro sun bi sahun ƴan bindigar tare da kashe da dama daga cikinsu.

Karanta Wannan  Yadda Aka Kama Mace Mai Jagorantar Maza Zuwa Satar Wayoyi A Kano

“Hankali ya fara kwanciya zuwa yanzu. Ana kuma ƙoƙarin mayar da sauran dabbobi da aka ƙwato daga hannunsu,” in ji Gulma.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta girke jami’an tsaro da yawa a yankin tare da jan hankalin mutane wajen sanar da wuraren da suka san mayaƙan na ɓoyewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *