
Rahotanni sun bayyana cewa jihohin Legas da Kano ne kan gaba wajan yawan masu rijistar katin zama dan kasa NIN.
Yawan wanda suka yi rijistar a Najeriya sun kai Miliyan 118.4.
Legas ce kan gaba wajan yawan masu rijistar inda take da mutane miliyan 12.7 da suka yi rijistar.
Sai kuma jihar Kano ta zo ta biyu inda take da mutane miliyan 10.4 kamar yanda hukumar kididdigar kasa ta NBS ta bayyana.
Kaduna ce ta zo ta 3 da mutane miliyan 6.9 da suka yi rijista.
Sauran jihohin na da mutanen da suka yi rijista kamar haka:
Ogun mutane 4.9 million
Oyo Mutane 4.5 million
Katsina Mutane 4 million
FCT Mutane 3.8 million
Rivers 3.5 million
Delta 3.2 million
Jigawa 3.1 million.
Imo 2 million
Kwara 2 million
Enugu 1.9 million
Kogi 1.9 million
Yobe 1.8 million
Taraba 1.7 million
Cross River 1.4 million
Ekiti 1.1 million
Ebonyi 999,991
Bayelsa 767,620.