Friday, December 26
Shadow

Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta janye yajin aikin gargaɗi da ta fara ranar Juma’a sakamakon ƙorafe-ƙorafen da suka shafi rashin kulawa daga ɓangaren gwamnati.

Wata sanarwa da ƙungiyar Nigerian Association of Resident Doctors (Nard) ta fitar ta ce ta janye yajin aikin na kwana biyar ne bayan gwamnatin Najeriya ta amince da fara biyan wasu buƙatunsu.

“Bayan yunƙurin da gwamnati ta nuna na biyan wasu buƙatun da muka sanar, da kuma shirin fara biyan alawus ga ma’aikatan da ke bin bashi…mun amince mu janye yajin aikin daga ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa ta bai wa gwamnatin tarayyar wa’adin mako biyu domin aiwatar da alƙawuran da ta ɗauka.

Karanta Wannan  Matashi Ba Taliya Ko Ƴan Kuɗi Yake Buƙata Daga Wajen Ƴan Siyasa Ba Face A Gina Rayuwarsa-Inji Sanata Ahmad Babba Kaita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *