
Gwamnatin jihar Kwara ta koka da karancin Likitoci a jihar inda hukumomin jihar sukace duk likitoci da yawa sun tsere kasashen waje.
Shugaban hukumar kula da asibitoci na jihar, Abdulraheem Abdulmalik ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace a yanzu likitocin da suke dasu guda 99 ne maimakon 180 zuwa 200 da jihar Ke bukata.
Yace suna neman likitoci su dauka amma babu, yace a kwankin baya likitoci 3 da suka tsere daga jihar sun koma bakin aiki bayan da aka yi karin Albashi.
Yace babbar hanyar magance wanan matsala itace a samu a rika daukar nauyin dalibai suna koyan aikin likitanci inda daga baya sai su dawo su yiwa jihar aiki.