Saturday, November 8
Shadow

Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Gwamnatin jihar Kwara ta koka da karancin Likitoci a jihar inda hukumomin jihar sukace duk likitoci da yawa sun tsere kasashen waje.

Shugaban hukumar kula da asibitoci na jihar, Abdulraheem Abdulmalik ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Yace a yanzu likitocin da suke dasu guda 99 ne maimakon 180 zuwa 200 da jihar Ke bukata.

Yace suna neman likitoci su dauka amma babu, yace a kwankin baya likitoci 3 da suka tsere daga jihar sun koma bakin aiki bayan da aka yi karin Albashi.

Yace babbar hanyar magance wanan matsala itace a samu a rika daukar nauyin dalibai suna koyan aikin likitanci inda daga baya sai su dawo su yiwa jihar aiki.

Karanta Wannan  Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami'ar Bayero

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *