Friday, December 5
Shadow

Ma’aikata ne suka yi yawa a jihar mu shiyasa muka kasa biyan mafi karancin Albashi na 70,000 inji Gwamnan Borno, Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa, ma’aikata sun yi yawa a kananan hukumomin jihar Borno shiyasa ya kasa fara biyan ma’aikatan kananan hukumomin mafi karancin Albashi na Naira 70,000.

Gwamnan yace akwai ma’aikata 90,000 a kananan hukumomi 27 dake fadin jihar wanda yace sun yi yawa shiyasa ya kasa fara biyansu mafi karancin Albashi na Naira 70,000.

Hakan na zuwa ne kusan shekara daya tun bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa wabuwar dokar karin albashi ta mafi karancin Albashi zuwa Naira 70,000 a ranar July 29, 2024.

Gwamnan ya bayyana hakane ta bakin babban sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Modu Mustapha yayin wani taro a gidan gwamnatin jihar Borno.

Karanta Wannan  Manufofin Tinubu sun ƙara jefa miliyoyin ƴan Najeriya cikin talauci - Falana

Yace jihar Kano ta fisu yawa sosai amma ma’aikatan kananan hukumomin ta basu wuce mutane 30,000 ba a kananan hukumomi 44 da jihar ke dasu.

Yace misali karamar hukumar Maiduguri na samun kudi daga gwamnatin tarayya da suka kai Naira Miliyan 700 amma kuma ma’aikatan kananan hukumomin karamar hukumar na bukatar Naira Miliyan 778 dan biyan Albashi yace kuma ana bukatar kudin da za’a wa mutane ayyuka, dan haka yace abin ba me sauki bane.

Saidai Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya bukaci shuwagabannin kananan hukumomi a jihar da su nemo hanyar da za’a bi wajan biyan mafi karancin Albashin amma yace baya goyon bayan korar ma’aikata.

Karanta Wannan  Ni Bayera bene Musulmi, Kuma sai na tabbatar an fara amfani da shari'ar Musulunci a Jihohin Yarbawa saboda fiye da rabin yarbawa musulmai ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *