
Ƙungiyar ma’aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMET sun sanar da janye yajin aikin da suka fara ranar Laraba.
Ma’aikatan sun ɗauki matakin janye yajin aikin ne bayan wata ganawa da suka yi da ministan sufurin ƙasar, Festus Keyamo a Abuja yau Alhamis.
Yajin aikin da suka kira kan rashin ingantaccen albashi, ya haifar da cikas a filayen jiragen sama na cikin gida – inda fasinjoji da dama suka kasa yin balaguro.
Ma’aikatan sun kuma ce sun damu matuka ganin cewa ba aiwatar musu da albashi mafi ƙanƙanta da gwamnatin tarayya ta amince da shi ba.