
Rahotanni na cewa, ma’aikatan wutar lantarki na Abuja zasu tafi yajin aiki.
Ana sa ran lamarin zai saka mutanen jihohin Naija, Kogi, da Nasarawa cikin duhu.
Ma’aikatan kamfamin me suna (AEDC) sun bayyana cewa, zasu tsunduma yajin aikinne saboda kasa cika alkawuran da kamfanin ya dauka bayan da suka yi yajin aiki a watan Nuwamba na shekarar 2024.
A cikin sakon da suka aikawa hukumar kamfanin na AEDC sun Sanar da cewa wannan shine karo na karshe da zasu yi gargadi kuma a koda yaushe zasu iya tsunduma yajin aiki