Wednesday, November 19
Shadow

Kaso 72 na yara a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa da suka kammala makarantun Firamare basu iya karatu ba>>Inji UNICEF

Hukumar Lafiya ta yara ta majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana cewa, kaso 72 na yaran da suka kammala makarantun Firamare a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa basu iya karatu ba.

Wakilin hukumar a jihar, Joseph Senesie ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai inda yace yara da yawa ana hanasu samun ilimi yanda ya kamata.

Yace yara Miliyan 2 ne a yankin basa samun zuwa makaranta. Yace kuma kananan hukumomi 12 a jihohin Borno da Yobe sunce akwai yara da yawa da ba’awa allurar Rigakafi ba.

Yace a cikin yara 10, 3 ne kawai ake samun rijitar haihuwarsu a hukumance wanda hakan ke sa basa samun tallafin karatu, Abinci da sauransu.

Karanta Wannan  Jami'in Hukumar NSCDC ya yanke jiki ya fadi ya mutu jim kadan bayan da aka masa karin girma

Saidai ya jinjinawa Gwamnatin jihar Borno kan kokarin da take na samar da tallafi ga rayuwar yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *