Wednesday, January 15
Shadow

Madrid za ta tattauna da Nacho, Chelsea na zawarcin Sesko

Kyaftin ɗin Real Madrid da ya lashe gasar zakarun Turai, Nacho, mai shekara 34, zai gana da ƙungiyar domin tattauna makomarsa indan kwantiragin ɗan wasan na sifaniya ya ƙare a wannan bazarar. (The Athletic)

Chelsea na da ƙwarin gwiwar cewa za ta iya fafatawa da Arsenal a yunƙurin sayen ɗan wasan gaban Slovenia Benjamin Sesko mai shekara 21 daga RB Leipzig(Standard)

Arsenal na nazari kan ɗan wasan Girona da Ukraine Viktor Tsygankov, mai shekara 26, wanda AC Milan ke zawarci. (Sport)

Manchester United na sha’awar sayen dan wasan bayan Everton da Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, yayin da ta ke neman ƙarfafa ƴan wasanta na baya. Kuma tana zawarcin ɗan wasan baya na Juventus da Brazil Gleison Bremer, mai shekara 27, da ɗan wasan baya na Nice da Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 24. (Football Insider)

Karanta Wannan  Hotuna: Kafar dan wasan Manchester United, Kobbie Mainoo ta dauki hankula

West Ham na ƙoƙarin daƙile yunƙurin Bayer Leverkusen na sayen ɗan wasan Girona da Sifaniya Aleix Garcia, mai shekara 26. (Guardian)

Hammers kuma suna son sayen ɗan wasan Vitoria Guimaraes da Portugal Jota Silva, mai shekara 24. (Teamtalk)

Manchester United na shirin tattaunawa da ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 24, kafin yanke shawara kan makomarsa. Sancho ya taimaka wa Borussia Dortmund ta kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin zakarun Turai bayan da ya koma ƙungiyar a matsayin aro bayan samun bambancin ra’ayi da kocin United Erik ten Hag. (ESPN)

Tottenham za ta bar Djed Spence, mai shekara 23, ya koma Genoa kan kwantiragin dindindin bayan da ɗan wasan na Ingila ya yi zaman aro a kulob ɗin na Italiya. (Fabrizio Romano)

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: A hukumance Real Madrid ta sanar da ɗaukar ɗan wasa Kylian Mbappe a matsayi na kyauta

Birmingham City ta tattauna da tsohon kocin Chelsea da Everton Frank Lampard kan zama sabon kocinta. Lampard ya kuma tattauna da Burnley game da maye gurbin Vincent Kompany wanda ya koma Bayern Munich(Football Insider)

Ƙungiyar Besiktas na Turkiyya na zawarcin tsohon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, mai shekara 51. Solskjaer bai samu wani aiki ba tun da ya bar United a watan Nuwamba 2021. (Mirror)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *