
Shugaban kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajero ya koka da cewa, mafi yawanci gwamnonin Najeriya kan bar jihohinsu su je Abuja su tare.
Yace hakan na faruwane a yayin mutanen jihohin wadannan gwamnonin ke fama da wahalar rayuwa.
Ya bayyana hakane a wajan taron karawa juna sani da ya faru a Lokaja jihar Kogi.
Ajaero ya bayyana cewa, sun ziyarci yankuna 5 na Najeriya amma mafi yawanci duk sun iske gwamnonin basa nan sun tafi Abuja.
An yi taron na NLC ne a Lokoja dan ma’aikatan jihar su bayyana matsalolinsu dan a kaiwa Gwamnan jihar.