
A karo na biyu an sake samun wani ya fito ya bayyana cewa, Tabbas ana Luwadi da mutane a gidan yari na Goron Dutse, yace duk wanda yace ba’a yi ba gaskiya ya fada ba.
A baya dai an samu wani da ya fito ya fada wanda har aka aika hukumar Hisbah ta yi bincike inda tace ba gaskiya bane.
Saidai Shi wannan matashi da ya fito yanzu yace shi an taba tsareshi a gidan Gyara Halin kuma ko da kaishi aka yi, zai nuna masu yi.
Saurari Hirarsa:
Ko da Hisbah suka ce ba gaskiya bane maganar Luwadi da Mutane a Gidan Gyara Hali na Goron Dutse, Mutane da yawa basu yadda dasu ba.