Da zarar kin rasa budurcinki, babu wata hanya da a likitance aka santa da zaki iya dawo dashi.
Budurci kamar wani marfine a kofar farjin mace wanda yake yagewa a yayin da namiji ya sadu da ita ko ta yi aikin wahala da dai sauransu.
Saidai a gargajiyance, akwai magungunan da ake bayarwa wanda ake matsi dasu ko shafawa dake ikirarin cewa gaban mace zai iya matsewa kamar wadda bata taba rasa budurci ba.
Amma babu tabbaci akan hakan, shi budurci idan ya tafi baya dawowa.
Sannan akwai wadanda akewa tiyata wanda a turance ake cewa surgery wanda yana dawo da budurcin mace amma shima ba kamar na farko ba.