Sunday, February 8
Shadow

Maganin tari na gargajiya

Akwai magungunan tari na gargajiya da yawa. A wannan rubutun, zamu bayyana su daya bayan daya:

Ana hada maganin tari na gargajiya da Karas, Lemun Tsami, Suga da Zuma.

Yanda ake hadawa shine, a samu karas din a wanke sannan a daddatsashi.

A matse ruwan lemun tsamin a zubasu a mazubi daya da zuma da sukarin.

A barshi ya kai awa 24 a ajiye.

Sannan a fara sha karamin cokali kullun sau biyu a rana.

Ana kuma iya hada maganin Mura da Zuma da Albasa.

Ana yanka Albasar a saka cikin kwano, daga nan kuma sai a zuba zuma a saman Albasar.

A rufe a barshi yayi akalla awanni 12.

Bayan nan sai a fara sha.

Saidai yaro dan shekaru 2 baya sha, sannan me ciwon sugar kada ya rika sha da yawa.

Karanta Wannan  Ba'a fahimci Kalaman shugaban kasar Amurka Trump bane, Shifa Ba 'yan Najeriya yace zai kawowa Khari ba, 'yan Tà'àddà yace zai Yhaqa>>Inji Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *