
Mahaifin Herbert Wigwe me bankin Access Bank wanda ya mutu a hadarin jirgin sama a shekara data gabata ya kai jikarsa, Miss Otutochi Channel Wigwe me shekaru 26 kotu akan maganar rabon gado.
Mahaifin me suna Pastor Shyngle Wigwe dan shekaru 90 ya kai Otutochi da wasu kotu inda yake neman kotun data saka wani ya kula da dukiyar dan nasa.
A doka ana saka wani ya kula da dukiyar mamacine idan mamacin ya mutu be bar wasiyya ba.
Saidai zuwa yanzu, kotun bata amince masa akan wannan bujata ba