
Matashin mai sana’ar ɗaukan hoto ɗan asalin Jihar Yobe, wanda ya samu nasarar lashe kambun bajinta na Duniya kan sana’arsa, (Guinness World Record In Photography), Sa’idu Abdulrahman, ya gana da fitaccen ɗan ƙwallon ƙafan Najeriya, Captin Ahmed Musa MON.
Ganawar wadda ta gudana a jiya, matashin ya gabatar wa Captin ɗin kundin nasa na bajinta da ya samu bayan da ya yi nasarar ɗaukan hotuna 897 cikin mintuna 60.
Sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da rawar da za su taka wajen tallafa wa masu tasowa cikin ayyukan fasaha a Najeriya ta yadda su ma za su samu damar bayyanawa Duniya irin tasu ƙwarewar.
Matashin ya yaba da yadda ya samu Ahmed Musa a matsayin mutum mai nasara a Duniyar ƙwallon ƙafa wanda kuma a kullum yake ƙoƙarin tallafawa masu tasowa da ƙarfafa musu gwiwa.
“’Na ji daɗi da na samu damar ganawa da Ahmed Musa har ma muƙa ƙulla alaƙar yadda za mu bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da fasahohi a Najeriya ƙarƙashin shirin Future Initiative”. Sa’idu ya ce.
Ya kuma ƙara da godewa Captin Ahmed Musan bisa lokacinsa, hikimarsa da kuma karramawar da ya yi masa.