
Kwamitin da’a na majalisar Dattijai yayi watsi da korafin da Sanata Natasha Akpoti ta shigar gabansa inda take zargin cewa, kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata.
Sanata Natasha Akpoti a zaman majalisar a jiya, Laraba ta gabatar da korafi a hukumance gaban majalisar inda kakakin majalisar Godswill Akpabio wanda shine take zargi da neman yin lalata da ita yace mata ta mika takardar korafin inda a karshe yace a kai takardar gaban kwamitin da’a na majalisar.
Saidai a zaman Kwamitin da’a na majalisar, shugaban Kwamitin, Sanata Neda Imasuen ya bayyana cewa ba zasu saurari korafin na Sanata Natasha Akpoti ba saboda maganar na kotu.
Yace a dokar majalisa, duk maganar dake kotu, kwamtinsu ba zai tattaunata ba.
Saidai kamin a tashi daga zaman majalisar, Sanata Natasha Akpoti tace ba maganar zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio kan neman yin lalata da ita bace ke kotu, maganar da majalisar ta yi akanta ne na cewa tana saka kaya masu nuna tsiraicinta.
Saidai kwamitin bai saurari wannan korafin na sanata Natasha Akpoti ba.
Hakanan Sanata Neda Imasuen ya kara da cewa, Korafin da Sanata Natasha Akpoti ta shigar bai bi ka’ida ba kuma yasan cewa, shima kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio yasan da hakan amma dan kada abin ya jawo cece-kuce shiyasa kawai yace a kawo mana korafin.
Yace ka’idar da korafin na Sanata Natasha Akpoti ya take itace, a dokar majalisar Sanata ba zai iya gabatar da korafi akan kansa da kansa ba sannan kuma ya sakawa takardar hannu da kansa ba.
Yace a doka, wani sanata dabanne ya kamata ya gabatar da korafi akan sanatan dake da matsalar, yace dan haka shima wannan yasa ba zasu iya sauraren korafin na Sanata Natasha Akpoti ba.
Yace kuma suma sun gayyaci Sanata Natasha Akpoti ta zo gabansu kan rigimar farko ta canja gurin zama amma taki, inda yasan lauyoyinta ne suka hanata zuwa.
Yace amma duk da hala zasu ci gaba da shari’ar.