
Tsohon gwamna jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa majalisar tarayya bata ki amincewa dashi ba a matsayin minista.
Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya fasa bashi mukamin na minista.
El-Rufai ya bayyana hakanne a yayin ganawar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Maganar nada El-Rufai Minista dai itace abinda ta jawo har aka samu tsamin dangantaka tsakanin El-Rufai da gwamnatin Tinubu.