Friday, December 5
Shadow

Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta naɗa Dakta Bashir Aliyu a matsayin sabon shugaba

Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta bayyana mataimakin shugaban ta, Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar a matsayin sabon shugaba.

Sanarwar ta biyo bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah a ranar Litinin.

A wata sanarwa da babban sakataren majalisar, Malam Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu, ta bayyana rasuwar Sheik Hadiyatullah a matsayin babban rashi ba ga majalisar kadai ba har ma ga daukacin al’ummar musulmin Najeriya da ma wajenta.

Yayin da ya ke addu’ar Allah ya gafarta masa, Ahmed ya ce an nada Dakta Bashir daidai da tsarin mulki da kuma tsarin da aka kafa majalisar a kai.

Karanta Wannan  Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta>>Inji Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *