
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya bayyana cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kasance tamkar lalataccen jirgin sama, kuma ga dukkan alamu ba ta da karfin da za ta sa ya sake cin zaɓe a 2027.
Da ya ke magana kan guguwar sauya sheka da ta samu PDP, wanda na kwanan nan shi ne gwamnan jihar Delt, Sheriff Oborewori, wanda ya koma APC tare da magoya bayansa da dama, Fasto Eno ya yi nuni da cewa nan ba da jimawa ba jam’iyyar PDP za ta durkushe.
Da ya ke jawabi ga dimbin jama’a da suka yi tururuwa a dandalin Town Square na mazabar Ukanafun/Oruk Anam a jiya Talata gwamnan ya bayyana cewa shi ma zai bi sahun masu sauya sheka yayin da zaɓen 2027 ke karatowa.