Friday, December 5
Shadow

Majalisar Dattijai zata yi dokar saka ido da kula da ayyukan bankunan yanar gizo irin su Opay, Moniepoint da sauransu

Majalisar Dattijai na shirin yin sabuwar doka dan kula da ayyukan bankunan yanar gizo irin su Opay, Moniepoint da sauransu.

Dayake magana akan muhimmancin wannan doka, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa, an taba sace masa kudi a asusun bankinsa kuma inda aka tura kudaden Opay ne da Moniepoint.

Yace kuma basu da rassa a zahiri da mutum zai ce ya shigar da korafi.

dan haka akwai bukatar a yi dokar da zata saka ido a ayyukan da suke.

Ita kuma a nata bangaren, Sanata Natasha Akpoti ta bayyana cewa wai idan aka yi wannan doka zata taimakawa matasan Najeriya dake samun kudi ta yanar gizo su rika samu daidai da takwarorinsu na kasashen waje.

Karanta Wannan  Da Duminsa:A karshe dai majalisa ta amince da Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *