Thursday, February 6
Shadow

Karya kika min, ban taba cewa, Tinubu Barawo ba>>Nuhu Rubadu ya gayawa Naja’atu Muhammad inda yace ta tabbatar ta fito ta bashi Hakuri nan da kwanaki 7

Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, Maganar da Naja’atu Muhammad ta yi akan cewa ya taba cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu barawo ba gaskiya bane.

Bidiyon da ya watsu a Tiktok ya dauki hankula sosai inda akai ta martani kala-kala. Naja’atu Muhammad ta bayyana cewa, Nuhu Ribadu ya yi wannan magana ne a lokacin yana shugaban hukumar EFCC.

Saidai lauyan Nuhu Ribadu, Dr Ahmed Raji, SAN ya bayyana cewa maganar Naja’atu ba gaskiya bane kuma suna neman nan da kwana 7 ta fito ta bayar da hakuri.

Sun ce idan bata yi hakan ba, basu da zabi da ya wuce su kaita kotu.

Karanta Wannan  Bidiyon tsiraicin hafsat baby: Ji Abinda Sheikh Aminu Daurawa yayi da Bidiyon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *