
Majalisar wakilai na shirin yin sabuwar dokar da zata hana ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa zuwa Asibitin kudi da saka ‘ya’yansu makarantun kudi.
Zasu dauki wannan mataki ne dan farfado da Kimar ma’aikatun gwannatin.
Dan majalisar, Hon. Amobi Godwin Ogah ne ya gabatar da kudirin a ranar Talata.
Yace amfani da Asibitoci da makarantun gwamnati da ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa ke yi ne yasa na Gwamnatin ke lalacewa.
Ya nemi goyon bayan wannan sabon kudiri daga ‘yan Jarida dama sauran ‘yan Najeriya.