Monday, December 16
Shadow

Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Majalisar tarayya ta dakatar da duk wani aikin da take a ranar Laraba inda ta fara tantance sabbin ministocin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mika mata sunayensu.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya aikewa da majalisar sunayen sabbin ministocin da ya nada bayan da yawa majalisarsa ta zartaswa garanbawul, inda ya hade wasu ma’aikatun sannan ya kirkiri wasu ya kuma kori wasu ministoci sannan ya nada wasu sabbi.

Senator Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da fara tantance ministocin sannan sanata Abba Moro ya goya masa baya.

Daga nan ne sai aka karanto sunayen sabbin ministocin da za’a tantance wanda ciki akwai Dr. Nentewa Yilwatda a matsayin ministan jin kai da rage talauci, Sai kuma Muhammad Maigari Dingyadi a matsayin ministan ayyuka da kwadago, Sai kuma Bianca Odinaka Odumegu – Ojukwu a matsayin karamar ministar harkokin kasashen waje.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

Sauran sune Dr. Jumoke Oduwole a matsayin ministan kasuwanci da ci gaba, sai Idi Mukhtar Maiha a matsayin ministan kula da dabbobi da ci gabansu sai Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Atah a matsayin karamin ministan gidaje, Sai kuma Dr. Suwaiba Said Ahmad a matsayin karamar ministar ilimi.

Shugaba Tinubu ya bukaci gaggauta tantance ministocin nasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *