Friday, July 17
Shadow

Muna ci gaba da kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace kuma zuwa yanzu mun kashe Naira Biliyan 29 a wajan gyaran>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin samar da wutar lantarki na kasa, TCN ta bayyana cewa zuwa yanzu ta kashe Naira Biliyan 29.3 a wajan gyaran wutar Lantarkin data lalace.

Karafunan wutar lantarkin 266 ne aka lalata a duka fadin Najeriya.

Ciki hadda wanda ya faru kwanannan wanda ya shafi wasu jihohin Arewa.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, Najeriya na tafka asarar Dala Biliyan 26 duk shekara saboda matsalar lalacewar wutar lantarki.

A baya dai irin wannan matsala ta faru a jihohin Abuja, Lagos, Kano, Enugu, Bauchi, Port Harcourt, da yankin Benin.

Karanta Wannan  Sanata Natasha Akpoti ta kasa kawo hujjar cewa na nemeta da lalata shiyasa ta fara bani Hakuri, kumama inda zaku san sharri ne irin nasu na mata ta kulla min, bayan tace ne nemeta da lalata ta bini min je taruka da yawa har kasashen waje kuma har hotunan Selfie ta rika dauka dani>>Sanata Godswill Akpabio

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *