
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike yace makaho ne kawai zai ce shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu baya kokari.
Wike ya bayyana hakane yayin da yake ran gadin wasu ayyukan da ake gudanarwa a Abuja.
Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kawo ayyuka masu kyau da inganci Abuja inda yace kowa ya shaida hakan. Abuja ta canja.
Ya karkare da cewa, Makaho ne kadai zai ce Tinubu bai yi kokari ba.