Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa,Man fetur din da matatar man Dangote ke samarwa ba zai ishi Najeriya ba dan haka zata koma ta ci gaba da shigo da Man fetur daga kasashen waje dan cike gibin suran man fetur din da Dangote bai iya samarwa.
Kamfanin na NNPCL yace matatar man fetur ta Dangote ta basu Lita Miliyan 10.3 ta man fetur din
Me magana da yawun NNPCL, Olufemi Sonoye ya bayyana cewa, suna fuskantar karancin lita miliyan 65.
Yace tun a farko an yi tsammanin rika samun lita miliyan 25 ne a kullun daga matatar man ta Dangote amma hakan bai samu ba.
Itama dai kungiyar ‘yan Kasuwa masu zaman kansu, IPMAN ta hannun shugabanta, Abubakar Garima ta bayyana cewa, man na Dangote ba zai ishi Najeriya ba sai an ci gaba da shigo da man daga kasagen waje.