Thursday, October 3
Shadow

Man Fetur din matatar man Dangote ba zai ishi Najeriya ba dan haka zamu ci gaba da Shigo da man fetur daga kasar waje>>inji NNPCL da ‘yan kasuwar Man Fetur

Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa,Man fetur din da matatar man Dangote ke samarwa ba zai ishi Najeriya ba dan haka zata koma ta ci gaba da shigo da Man fetur daga kasashen waje dan cike gibin suran man fetur din da Dangote bai iya samarwa.

Kamfanin na NNPCL yace matatar man fetur ta Dangote ta basu Lita Miliyan 10.3 ta man fetur din

Me magana da yawun NNPCL, Olufemi Sonoye ya bayyana cewa, suna fuskantar karancin lita miliyan 65.

Yace tun a farko an yi tsammanin rika samun lita miliyan 25 ne a kullun daga matatar man ta Dangote amma hakan bai samu ba.

Karanta Wannan  Akwai yiyuwar a fada wahalar Man fetur saboda NNPCL tace bashi ya mata yawa

Itama dai kungiyar ‘yan Kasuwa masu zaman kansu, IPMAN ta hannun shugabanta, Abubakar Garima ta bayyana cewa, man na Dangote ba zai ishi Najeriya ba sai an ci gaba da shigo da man daga kasagen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *