
Manyan malaman kiristoci sun yi ruwan Allah wadai ga gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka bukaci da ya kawo hanyar kawar da matsalar tsaro data talauci da matsin tattalin arziki.
Sun bayyana hakanne a sakonnin bukukuwan Easter daban-daban da suka fitar.
Misali babban fasto, Bishop Matthew Hassan Kukah ya misalta halin da Najeriya ke ciki da lokacin da aka gicciye Yesu inda yace Tinubu ya sauko da mutanen Najeriya daga gicciyewar shedan.
Bishop Kuka yayi kira ga gwamnatin data dauki matakan gaggawa na kawo karshen matsalolin tsaro da yunwa da sauransu.
Yace mafi yawancin ‘yan Najeriya sun yanke tsammanin samun canji amma su a matsayinsu na kirista basu yanke tsammani ba.
Yace duk da ba Tinubu bane ya saka ‘yan Najeriya a cikin wannan hali ba amma yana Kiran ya kawo hanyar samun sauki ga ‘yan kasa.
Hakanan shima Fasto Tunde Bakare a sakonsa na ranar Lahadi ya caccaki gwamnatin ta Tinubu inda yace mutane sun fara gajiya da addu’a.
Yace dolene sai shuwagabanni sun tashi tsaye sun dauki matakan kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da ita.
Ya bayyana jihohin Filato da Benue a matsayin wadanda suka fi fama da wannan matsalar tsaro.
Ya yi kiran da a dauki matakin gyara tun kamin a akai Talaka wuya.